BOC - Wasika Zuwa Sama

Mutuwa... mutuwa
Mutuwa... mutuwa

Baba...
Mutuwar Ka Bai Zo Mana Da Sauki Ba
Abun Takaicin Ma
Shi Ne Da Mun Wuce Mutan Anguwa Suna Hira
Maimakon Mun Jaje Da Tausaya Wa Yanayi Na
Sai Ka Ji Sun Ce Na Chacchanci Azaban Da Ke Bi Na
Kullum Mama Tana Cikin Tunani
Sun Ki Barin Ta Ta Huta
Suna Ta Kiran Ta Maiya
Ba Fada Mun Aka Yi Ba Na Ji Na Gani Da Kai Na
Ya Zan Yi Da Rai Na
Duk Da Dai Da Sanin Mu Cewa Da Kudin Ka Ka Gina
Baba Karami Sun Zo Sun Kore Mu Sun Sai Da Gidan
Wai Don Mama Ba Ta Taba Haifan Yaro Na Miji Ba
Kuma A Al’adan Ku Ba A Raba Gado Da Iri Na
Sai Ka Ce Ni Na Hallaci Kai Na ‘Ya Mace
Ashe, Rayuwar Wassu Marayu Haka Ne
I’m In Pain Hoping For Better Days
While I Pray You Are In A Better Place

Mutuwa... mutuwa
Mutuwa... mutuwa

Mama...
Mutuwar Ki Ya Bar Mu Cikin Azaba
Ba Mu Samun Kula A Kan Kari Yadda Muka Saba
Barin Ma An Daina Sa Mana Abincin Mu Da Nama
Mun Daina Zuwa Makaranta Don Bamu Samun Dama
Daga Dan Gaban Goshin Ki Yanzu Ni Ne Bawar Gidan
An Sallami Baba Mai Aiki...
Ni Ne Na Mai Da Gurbin Ta Sai Dai Ni Din Ba A Biya
Da Safe Ni Na Kan Riga Kowa Tashi
Da Dare, Kowa Ya Kan Riga Ni Barci
Kanne Na Duk Sun Koma Zama Da Kawu A Kauye
Duk A Bayan Mutuwar Ki Don Baba Ya Sake Aure
Mun Yi Matukar Rashi
Fiye Da Manomin Da Bayan Damina Mai Albarka Wuta Ya Kone Masa Hatsi
Oh Mutuwa! Ya Sace Mu Wane Dan Fashi
Da So Shi Ne Samu, Ki Dawo Rayuwa Ko Na Minti Daya In Gan Ki
Wasika Daga Dan Ki

Mutuwa... mutuwa
Mutuwa... mutuwa

Da Na Makadaici
Mutuwar Ka Ya Faru Ne Kamar A Mafarki
Ko Zan Gan Ka A Raye In Na Farka Daga Barci
Ka Tafi Ka Bar Mutan Duniya Na Ta Mun Habaici
Kullum Ina Cikin Tamabaya...
Shin Ta Wani Hanya Na Yi Wa Rayuwa Laifi
Ji Nake Kamar Ni Ne ‘Yar, Kai Ne Mahaifi
Da Safe In Zan Fita Wa Zai Ce Mun Sai Anjima
-Wa Zai Ce Mun Maraba In Na Dawo Da Maraici
Wa Zai Haifa Mini Jika?
Wai Zai Ce Mun Yana So?.. Wa Zai Karba In Na Mika?
Tunda Mahaifin Ka Ma Ba Ya Nan Wa Zai Mini Hira
Wai Karfafa Ni,Wa Zai Gina Mini Gida
Tun Ranar Da Na Haife Ka Na San Zaka Zamo Soja
Har Hakan Ya Zamo Gaske
-Ka Yi Nasara A Yakin Farko, Ka Dawo… Daka Koma
Labarin Mutuwan Ka Ne Ya Kwankwasa Mini Kofa
Wish I Stopped The Bullet
Wish I Had Made The Trigger Disappear Before They Pull It

Mutuwa... mutuwa
Mutuwa... mutuwa