Yana da nashi lokaci
Yana da nashi....
Komai na da lokaci... komai na da lokaci
Yana da nashi lokaci... yana da nashi lokaci
Komai na da lokaci... komai na da lokaci
Yana da nashi lokaci... yana da nashi lokaci
Komai na duniya bishi sannu lokaci ne
Da ma an fada mahakurci ai mawadaci ne
Tapi a sannu sannu zaka je ai gaskiya ne
Sauri kake tayi wai ina zaka je ne
Kar fa ka manta shi gaggawa aykin shaidan ne
Idan kay tunani ay shekara ma kwana ne
Sannan yau da gobe dukkan ninshi na Allah ne
Komai kake so iy haquri zaezo lokaci ne
A kwana a tashi wattaran bafade sarki ne
Waye yace durkusawa wada gajiyawa ne
Maza lura da harshenka alqalin zance ne
Kar fa ka manta kowa a gidansu sarki ne
Na ji ance tuwon girma miyansa na nama ne
Kowa a duniya da irin baewansa ku gane
Wani shi malamine wani shiko mawaqi ne
Wancan dan kasuwa ne wancan ko maggini ne...
Komai na da lokaci... komai na da lokaci
Yana da nashi lokaci... yana da nashi lokaci
Komai na da lokaci... komai na da lokaci
Yana da nashi lokaci... yana da nashi lokaci
Karda ka bar aykinka kace zaka dau na wane
Kowa ya tsaya a nasa kama da wane bashi wane
Kowa da yannayinsa raayi shi riga ne
Ai hippop ta kowa ce ba wance ba wane
Abinda na yarda dashi ni dai kawai guda ne
Wannan maikoyo ne waccn ko shi gwani ne
A kwan a atashi mai koyo ai malami ne
Masoyan gaskiya gani wai kuna ina ne
Domin yaba kyauta a ko ina ay tukuici ne
Mai baka shawaran kirki gani na dan uwa ne
Kaso a soka ako ina hakan ai daidaine
A hadu azo a zauna ai hakanma ar xiqi ne
Nagode Allah
Na qara gode Allah... hahaha (Queen ZeeShaq)
Komai na da lokaci... komai na da lokaci
Yana da nashi lokaci... yana da nashi lokaci
Komai na da lokaci... komai na da lokaci
Yana da nashi lokaci... yana da nashi lokaci
Yor komai lokaci ne a duniya
Kabi sannu komai zai wuce
Gaesuwa ta musamman
Ga sister na Aisha... AleeGee
M J... UniquePikin... JNaz
AbbaFido... K B Teku
Kowa da kowa Ana Tare
B Mary komai lokaci ne...
Wagga Billy’O ne yake magana